Hukumar NASA ta yada hotunan naurar bincike mai suna "Perseverance" da ta aika duniyar Mars.
Na'urar "Perseverance" da ka sarrafa da na'urar daukar hoton Mastcam-Z mai faifai 142 an yadfa yadda yake aiki a shafukan yanar gizon NASA/
An harba na'urar Perseverance ne a ranar 30 ga watan Yunin 2020 daga filin harba na'uarorin sararun samaniya dake birnin Florida wanda ya kwashe watanni 7 ya na tafiyar kilomita miliyan 470 gabanin ya sauka a duniya Mars a ranar 20 ga watan Febrairu.
Na'urar "Perseverance" mai amfani da man plutonium da aka yi a dakin binciken NASA mai suna Jet Propulsion kawo yanzu ya kasance na'uarar sararin samaniya mai bincike a duniyar Mars mafi inganci a fannin kimiyya.