Shugaba Zelensky ya ce, zai gabatar da shirin cimma zaman lafiyar tsakanin ƙasashen biyu ga takwaransa na Amurka Joe Biden da kuma mutane biyu da ka iya zama magajin Biden ɗin nan kusa.
A yayin zantawarsa da manema labarai, Zelensky ya ce, mamayar makwanni uku da sojojinsa suka yi a Kursk na Rasha na cikin shirin da ya ce zai gabatar, amma kuma akwai wasu batutuwa da suka danganci tattalin arziki da diflmasiya da zai muhimmanta a cewarsa.
Zelensky ya ce, babbar mnufar wannan shirin ita ce tilasta wa Rasha kawo karshen yakin wanda aka fara shi tun watan Fabairun 2022.
Kodayake Zelensky bai yi cikakken bayani ba game da shirin da ya ce zai gabatar, illa kawai ya jaddada cewa, zai tattauna batun da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta Jam’iyyar Democrat da kuma watakila Donald Trump na jam’iyyar Republican, wato ƴan takara biyu da ake sa ran ɗaya daga cikinsu zai zama shugaban ƙasa.
Shugaban na Ukraine ya ce, yana fatan ziyartar Amurka cikin watan gobe na Satumba domin halartar babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI