Wata yar kasar Kanada mai suna Jenny Molendyk Divleli wacce ta karbi Musulunci a shekarar 2006 ta samar da wata hanya mai sauki na koyawa yara addinin Islama.
Molendyk wacce ke zaune a Istanbul a halin yanzu Malaman yaren Ingilishi ne wacce ta fara amfani da basirarta wajen koyawa yara addinin Musulunci ta bidiyon koyarwa da take yadawa a kafafen sadar da zubunta da take yi da yaranta biyar.
Bidiyon da take yadawan suna kunshe da dabarun koyarwa iri daban-daban wadanda ke koyar da Islama ga yara musamman yaruwar Annobi Muhammadu (SAW)
Kamar yadda jaridar Daily Sabah ta rawaito, a hirar da ta yi da kanfanin dillancin labaran Anadolu, Molendyk ta bayyana cewa mahaifinta dan sanda ne, mahaifiyarta kuwa naz ce kuma dukkaninsu Kirista ne.
A yayinda ta yanke hukuncin karbar addinin Islama ta samu kalubale daga mahaifinta amma hakan bai sanya ta sauya ra’ayinta ba.
Bayan ta gudanar da bincike sosai ta yanke hukuncin karbar addinin Islama a ranar 14 ga watan Mayun 2006. Ta kuma hadu da Sami Divleli wanda ta aura daga bisani suka koma Istanbul a shekarar 2012.
Molendyk ta bayyana cewa karbar Musulunci ya gyara mata rayuwa inda ta jaddada cewa "Na gano cewa Musulunci shine hanya madaidaiciya,