Sojojin da suka karbi ragamar mulki bayan juyin mulkin soja da suka gudanar a Myammar sun nemi taimako daga Firaministan Thailand, Prayut Chan-oca domin hanzarta aikin komawa ga dimokiradiyya.
Firaministan Thailand, Prayut Chan-oca ya ce ya samu wasika daga Janar Min Aung Hlaing, shugaban gwamnatin wucin gadi.
A cikin wasikar, Prayut ya yi nuni da cewa Janar Hlaing ya nemi gwamnatin Thailand da ta taimaka wajen tallafawa dimokiradiyya a Myanmar.
Ya ce "Muna goyon bayan tsarin dimokiradiyya a Myammar, amma muhimmin abu a gare mu a yanzu shi ne kare dangantakarmu da kasar."
Firaministan Thailand, Prayut ya karbi mulki daga Firaminista Yingluck Shinavatra a shekarar 2014 kuma ya ci gaba da rike mulki bayan babban zaben da aka gudanar a 2019.