Pelicot mai shekaru 71 ya fada komar 'yan sanda ne lokacin da aka kama shi saboda zargin hayar mutane ta kafar intanet domin zuwa su ci zarafin matarsa ta hanyar fyade.
Bayanan 'yan sanda sun ce wanda ake zargin na bai wa matar tasa sinadarin da zai kawar da hankalinta ne kafin sanya bakin da ya dauko yin lalata da ita.
Yayin da yake amsa tambayoyi a gaban kotu yau talata, Pelicot ya ce babu banbanci tsakaninsa da sauran mutane 50 da ya sa suka yiwa iyalin nasa fyade, saboda haka yana neman gafara daga wurinta.
Wanda ake zargin ya ce duk wadanda ya dauko hayarsu domin lalata da matar tasa sun san cewa fyade za su yi, kuma ya yi nadamar laifin da ya aikata.
Uwargidan Pelicot, Gisele ta bukaci a gudanar da shari'ar a bainar jama'a domin kowa y asan abinda ya faru da kuma irin matakan da suka dace a dauka domin kare hakkokin mata.
Daga cikin tuhume tuhumen da ake yiwa Pelicot harda kwashe shekaru kusan 9 tsakanin shekarar 2011 zuwa 2020 na sanya mata sinadarin dake kawar mata da hankali domin bada damar yi mata fyaden a kauyen Mazan dake kasar ta Faransa.
Pelicot ya amsa laifuffukan da aka tuhume shi a kai a cikin wannan shari'ar da ta dauke hankalin jama'a, ya yin da ya bayyana cewar ya ta shi ne a cikin irin wannan mummunan yanayin inda iyayensa ke cin zarafin juna.
Pelicot ya roki matar tasa da 'yayansa da kuma jikokinsa da su masa aikin gafara, ya yin da ake ci gaba da gudanar da shari'ar.
Matar ta sa ta yi nasarar samun takardar saki a watan jiya, ya yin da tace bata taba tunanin mijin da suka kwashe shekaru 50 suna tare zai mata irin wannan cin zarafi ba.
Gisele ta ce kafin aukuwar wannan lamari tana iya sadaukar da ran ta domin kare tsohon mijin na ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI