An sanar da cewa mutum uku ne suka rasa rayukansu sakamakon faduwar wani karamin jirgi a garin Detroit dake jihar Michigan a kasar Amurka.
A cikin jirgin dai tare da matukinsa da wasu mutum biyu duk sun rasa rayukansu.
Jirgin dai ya fada akan wani dakin wani gida da aka yi sa'a babu kowa a ciki a wannan lokacin.
Gobara dai ta kama wani barayin gidan lamarin da masu kashe gobara suka magance nan take.