Sanarwar da shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya Volker Turk ya fitar a talatan nan na cewa akalla mutane 901 aka zartas da hukuncin kisa a kansu cikin shekarar 2024, sannan ya ce abin tashin hankali ne yadda a kusan kowacce shekara adadin masu fuskantar hukuncin ke karuwa a Iran.
Shugaban ya kuma ce lokaci ya yi Iran ta rage daukar tsatsaurar hukuncin nan a kan mutanen da ta ke kamawa da aikata laifukan da suka hada da safarar muggan kwayoyi, ko kuma fyade ko cin zarafi ta hanyar neman yin lalata ko kuma kisa.
Baya ga China da ya zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da ta ke aiwatar da hukuncin kisa a kan su ba, Iran ce kasar da ke kan gaba wajen kashe masu aikata manyan laifuka a kowacce shekara, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil adama ciki har da amnesty international suka tabbatar.
Masu fafutuka dai na cigaba da kokawa da yawaitar rataye masu laifi a Iran, inda suka zargi hukumomi karkashin mulkin Ayatollah Ali Khamenei da yin amfani da wannan mataki wajen saka tsoro a zukatan al’umma, musamman biyo bayan zanga zangar gama gari da ya gudana a kasar tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI