Mutum miliyan 30 aka yiwa allurar riga-kafin Korona a Turkiyya

Mutum miliyan 30 aka yiwa allurar riga-kafin Korona a Turkiyya

A kasar Turkiyya an bayyana cewa an yi alluran riga-kafin Korona har kwara miliyan 30.

Ministan lafiyar kasar Turkiyya Fahrettin Koca ya sanar da matakin da aka cimma a yin allurar riga-kafin Korona a shafin sa na sada zumunta.

Minista Koca ya bayyana cewa ya zuwa yau, allurai miliyan 30 aka yi.

Da yake nuna cewa samar da allurar rigakafin za ta ci gaba ba yankewa, Koca ya ce,

"Fiye da kashi daya bisa uku na jama'ar mu an yi musu rigakafin. Mun yi yarjejeniya fiye da sau ukun yawan al'umman kasarmu na yawan alurar rigakafin yawan mu. Gobe zai fi na yau kyau."


News Source:   ()