Kawo yanzu a yayinda kwayar cutar Corona ta yi ajalin mutane dubu 841 da darı 486, wadanda suka kamu da ita sun kai miliyan 24 da dubu 920 da 25, yawan wadanda kuma suka warke ya kai miliyan 17 da dubu 303 da dari 818 a doron kasa.
A kasar Indiya wadanda cutar ta kashe a cikin awanni 24 da suka gabata sun kai dubu 1 da 21, a jumlace mutum dubu 62 da 750 suka rasa raykansu a kasar. Yawan wadanada suka kamu da cutar a kasar kuwa sun kai miliya 3 da dubu 468 da 272.
A nahiyar Afirka a cikin awanni 24 an samu karin mutum 231 da suka rasa rayukansu a jumlace mutum dubu 29 da 141 cutar ta yi ajali a nahiyar. A nahiyar dai a kasar Afirka ta Kudu aka fi samun yawan mace-mace sanadiyar cutar inda a jumalace mutum dubu 13 da dari 743 suka rasa rayukansu, sai kasar Misira da dubu 5 da dari 362 sai kuma kasar Aljeriya da dubu 1 da dari 483.
A cikin awanni 24 an samu karin mutun 9 dauke da cutar a China, 323 kuma a Koriya ta Kudu.