Gidan adana kayan tarihi na Mevlana da ke Konya, inda kabarin Mevlana Celaleddin Rumi yake, daya daga cikin manyan sufayen duniyar Turkiyya da Musulunci , yana maraba da baki daga ko'ina a fadin duniya.
Adadin masu yawon bude ido na cikin gida da na waje da suka ziyarci gidan tarihin a cikin watanni 8 na wannan shekara ya kai dubu 650.
Sakamakon dokokin da aka sanya saboda sabon nau'in cutar coronavirus (Covid-19) wanda ya shafi duniya baki daya, mutane miliyan 1 ne kawai suka ziyarci Gidan Tarihin Mevlana a 2020.
Ana sa ran adadin masu ziyarar zai zarce miliyan 1 a bana.