Mutum daya ya rasa ransa yayin da biyu suka bace sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku sanadiyar ruwan sama mai karfin gaske a China.
Mutane da yawa suma sun tagayyara sabili da ruwan sama kamar da bakin kwarya a lardin Henan.
Babban birnin lardin, Zhengzhou, na daya daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa.
An tura karin kungiyoyin bincike da ceto daga jihar zuwa yankin.