An sanar da mutuwar mutum daya da runanan wasu hudu a harin wuka da aka kai a Amsterdam, babban birnin kasar Holan.
A wata sanarwa da ‘yan sandan Amsterdam suka fitar a shafin Twitter, an bayyana cewa wani mutum da wuka ya kai hari kan mutane 5 a Ferdinand Bolstraat.
An sanar da cewa daya daga cikin wadanda aka kaiwa harin ya mutu a wurin kuma mutane 4 da suka jikkata suna asibiti, an dai yi nasarar kama maharin tare da tsare shi.
'Yan sanda ba su fitar da bayanai game da asalin maharin mai shekaru 29 ba.