Wani harin ta'addancin bam da aka kai kusa da wani Masallaci dake jihar Kandahar a kudancin Afganistan ya yi sanadiyar rayukan mutum biyu.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Tarık Aryen ya sanar da cewa bam din da aka ajiye a gaban Masallacin Abdul Aziz a yankin Ainu Mine dake Kandahar ya fashe a yayinda farar hula ke wucewa.
Harin ya yi sanadiyar rayuka biyu da kuma raunana wasu farar hula uku. An kuma dora alhakin kai harin akan kungiyar Taliban kamar yadda Aryen ya bayyana.
Kawo yanzu dai Taliban ta bace komai game da lamarin ba.