An sanar da cewa harin da wani ya kai da wuka a kusa da wani tasar jirgin kasa a birnin New York a kasar Amurka ya yi sanadiyar rayukan mutane biyu da raunana wasu biyu kuma.
An sanar da cewa a kusa da layin dogon da aka kai harin wanda ya kai harin ya sake yunkurin kai harin a gurin bayan 'yan sa'o'i kadan da harin farko.
Tun dai an aika da 'yan sanda 500 a yankin tare da duba kamarar tsaron yankin da zummar kama wanda ya aikata aika-aikan.