An gudanar da allurar rigakafin coronavirus sama da biliyan 3.57 a duk duniya, a cewar wata kididdiga ta kafar yanar gizo mai alaka da Jami'ar Oxford.
China ce kan gaba a fadin duniya da sama da allurar rigakafin Korona biliyan 1.43, sai Indiya da ke biye da miliyan 395.34.
Jerin ya ci gaba da yawancin kasashen Yammacin Turai, inda Amurka ta yi allurai miliyan 336.05, Brazil miliyan 120.73, Jamus miliyan 84.99, Birtaniya miliyan 81.44, Japan miliyan 66.71, da Faransa miliyan 62.32.
Turkiyya ta kasance ta tara akan jerin da tayi sama da miliyan 61.81, sannan Italy, Indonesiya, da Mexico.
Kasar da ta fi ayyanar da yawan allurar riga-kafin idan aka kamanta da yawan al'umman kasar jama'a ita ce Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da allurai 163.74 cikin mutum 100 bisa ga lissafin ko wane mutum daya zai iya karbar allurar biyu.
Bayan Hadaddiyar Daular Larabawa sai kasashen tsibirin Malta tare da 162.71 allurai a cikin kowane mutum 100 da Seychelles mai 141.98, Iceland 136.68, San Marino 132.74, Bahrain 130.76, Uruguay 128.35, Chile 126.85, Isra'ila 126.62, Katar 120.61, Faroe Islands 120.42, Birtaniya 119.96, Mongolia 119.36, da Kanada 117.36.