Mutane 81 ne suka rasa rayukansu sakamakon bala'in ambaliyar ruwa a Yankin yammacin Bahar Maliya a ranar 11 ga watan Agusta.
Shugaban Hukumar Kula da Bala'i da Agajin Gaggawa (AFAD) ya sanar da cewa mutane 16 sun bace, 10 a Kastamonu sai 6 a Sinop.
Ana ci gaba da kokarin ba tare da katsewa ba don gano wadanda suka bace.