An sanar da kashe mutum takwas a wani harin da aka kai a tashar jirgin ruwan Hodeida dake kasar Yaman.
An samu karin fadace-fadace a kusa da tashar jirgin ruwan inda Matakan Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kange faruwar yaki tsakanin dakarun gwamnatin da Saudiyya ke jagoranta da mayakan Houthi.
An dai zargi mayakan Houthi da laifin kai harin da ya yi sanadiyar rayuka takwas a yankin tashar jirgin ruwan
Ministan sadarwar kasar Yaman Moammar Al-Eryani ya yi tir da Allaha wadai akan harin da yake zargin mayakan Houthis ne suka kai a yankin da ‘yan Uwa Thabit suke.