Mutane 7 sun mutu sakamakon nitsewar jirgin ruwan da ke dauke da bakin haure a kusa da tsibirin Lampedusa da ke kudancin Italiya.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya a gabar tekun tsibirin Lampedusa, yanki mafi kusa da Afirka a cikin Tekun Bahar Rum.
A cewar labaran kamfanin dillancin labarai na ANSA, bakin haure 7 har da wata mai juna biyu sun rasa rayukansu a cikin jirgin ruwan da ya nitse a mil 5 daga Lampedusa.
An bayyana cewa, jami'an tsaron gabar tekun Italiya da suka kai dauki sun kubutar da mutane 48 sannan mutane 9 sun bace.
An sanar da cewa an kai gawarwakin bakin hauren 7 tare da wadanda aka ceto Lampedusa.
Bakin hauren da suka bayyana a yankin a cikin yan kwanakin da suka gabata daga kasashen Arewacin Afirka sun kai 660.