Mutane 7 ne suka mutu yayin da 17 suka jikkata a harin da kungiyar ta'adda ta DAESH ta kai a tantin ta'aziyya a Iraki.
An kai harin ta'addanci a garin Salahaddin dake Iraki. 'Yan ta'addar DAESH sun kai farmaki a wajen da ake zaman makoki.
An kashe mutane 7 yayin da 17 suka jikkata a harin. An sanar da cewa an kaddamar da farmaki kan kungiyar ta'adda a yankin.
DAESH ta kuma kai hari a wata kasuwa a Bagadaza babban birnin kasar a makon da ya gabata. Mutane 35 sun mutu a harin da suka kai da bam.