An sanar da cewa harin kunar bakin wake da aka kai da bam a babban birni Somaliya Mogadishu da kuma birnin Baidoa ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyar da raunana wasu 15.
Mai magana da yawun jami'an 'yan sanadn Somaliya Sadik Aden Ali ya shaidawa manema labarai da cewa an kai harin na farko ne a ginar hukumar kwastan dake filin tasar jirgiin ruwan Mogadishu, hari na biyu kuwa an kai shi ne a wani gidan siyar da abinci dake birnin Baidoa.
A harin da aka kai Mogadishu a yayinda jami'an tsaro suka yi yunkurin dakatar da maharin ya tayar da bam din dake jikinsa, baya ga maharin babu wanda ya rasa ransa sai dai jami'an tsaro biyar sun raunana.
A harin birnin Baidoa kuwa mutum biyar suka rasa rayukansu inda 10 suka raunana.