A Kenya, sojoji 17 sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu mallakar rundunar sojin kasar.
An bayyana cewa, akwai mutane 23 a cikin jirgin helikofta na soja da ya fadi a yankin Kajiado na Nairobi babban birnin kasar da safe kuma helikofta ya tashi ne da nufin horas da wasu sojoji.
An tabbatar da cewa sojoji 17 a cikin jirgin mai saukar ungulu sun mutu sannan sojoji 6 sun ji rauni.
A gefe guda kuma, yayin da sojojin Kenya suka tabbatar da faduwar jirgin mai saukar ungulu, ba su bayar da bayanai kan adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata ba.