Mutum 15 sun mutu a turmutsutsun da ya afku a wurin taron addinin Hindu a Indiya

Mutum 15 sun mutu a turmutsutsun da ya afku a wurin taron addinin Hindu a Indiya

Tuni Firaminista Narendra Modi ya aike da sakon ta'aziya ga iyalan waɗanda haɗarin ya ritsa da su.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan turmutsutsun ba a bukukuwan addinin mabiya Hindu da ke gudana a Kumbh Mela ta kasar India, wanda ke samun halartar mutane akalla miliyan 4 kowaccce shekara.

Rahotanni sun ce an samu hadarin na yau da asubah lokacin da dubban mutane suka kwarara domin yin wanka a kogin Ganges wanda ake girmama ruwansa, inda suka dinga take mutanen da ke bacci kusa da shi.

Wani daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya, Renu Devi, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar mutane da dama ne suka danne shi amma Allah ya kubutar da shi.

Devi ya ce dattawa da mata da dama sun mutu saboda babu wanda ya kai musu ɗauki lokacin da lamarin ya auku.

Wani likita a asibitin wucin gadi na garin ya tabbatar da mutuwar akalla mutane 15, tare da samun wasu da dama da suka samu raunuka daban-daban.

Yau Laraba na ɗaya daga cikin ranaku masu daraja ga mabiya addinin Hindu da ke halartar wannan ibada, inda limaman su ke jagorantar mahalarta wajen wanka a wannan kogi na Ganges mai daraja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)