Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Turkiyya Dkt. Fahrettin Koca ya bayyana cewa a halın yanzu mutum 113 ne kawai ke kwance a asibiti sanadiyar fama da Covid-19 a fadin kasar.
A ranar 26 ga watan Yuni marasa lafiya 1,492 aka samu sun warke inda yawan ya dan haura wadanda aka samu ta cutar a ranar.
A bisa haka a ranar Juma’ar ayayinda mutum 1,492 suka warke daga cutar, mutum 1,396 aka samu dauke da ita.
Kawo yanzu dai a fadin kasar Turkiyya an yiwa mutum miliyan 3,186,622 gwajin kwayar cutar ta Covid-19, daga cikinsu an samu dubu 194,511 dauke da cutar, daga cikin wadanda ke dauke da cutar dubu 167,198 sun warke inda kuma dubu 5,065 suka rigamu gidan gaskiya.