Mutum 100 sun rasa rayukansu a harin ta'addanci da aka kai Burkina Faso

Mutum 100 sun rasa rayukansu a harin ta'addanci da aka kai Burkina Faso

Akalla fararen hula 100 aka kashe a wani harin ta'addanci da aka kai a wani kauye da ke arewacin Burkina Faso.

A cewar  kamfanin dillacin labaran kasar Burkina Faso ta AIB, ‘yan ta’addan da suka je kauyen Yaghga da ke arewacin yankin Sahel da daddare sun bude wuta kan mazauna kauyen.

Maharan sun kuma kona gidaje da kasuwar mutanen yankin.

Akalla mutane 100 suka mutu a harin ta’addancin. Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu.

Shugaba Roch Kabore ya ayyana zaman makoki na kwana uku wanda zai fara a daren yau.

Tun a shekarar 2015 ne kasar ta Burkina Faso take fuskantar hare-haren ta'addanci.

A cewar bayanan Majalisar Dinkin Duniya, mutane miliyan 1.1 sun yi gudun hijira a cikin kasar saboda hare-haren da ake kaiwa fararen hula a kasar.


News Source:   ()