An bayyana mutuwar mutum 1 sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 7,3 da ta afku a yankin Fukushima na arewa maso-gabashin Japan a ranar 13 ga Fabrairu.
Gwamnatin Fukushima ta sanar da rasa rai na farko sakamakon girgizar kasar mai karfin awo 7,3 da ta afku.
Sanarwar ta ce, wani mutum ma shekaru 50 da abokinsa ya nema ya rasa tsawon kwanaki, ya gano gawar sa a karkashin wata durowa da ya buya don kare kansa.
A gefe guda, Hukumar Kashe Gobara da Yaki da Ibtila'o'i ta sanar da jikkatar mutane 185 da lalacewar gidaje dubu 3,112 a jihohi 10 da ke arewa maso-gabashin Japan.
An jiyo motsawar kasa a garuruwan Miyagi, Iwate, Akita, Gunma, Saitama, Aomori da Tokyo Babban Birnin Japan.