Bayan nazarin da aka sake yi kan adadin mutanen da cutar Corona ta yi ajali a kasar Ecuador da ke Kudancin Amurka, an gano adadin ya karu da mutane dubu 8,786 wanda ya kawo jimillar wadanda suka mutu zuwa dubu 30,744.
Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta Ecuador ta fitar ta bayyana cewa, an gano mutanen da suke dauke da alamaun kamuwa da Corona amma kuma ba a dauki bayanansu ba, wanda hakan ya sanya aka sake lissafa adadin wadanda annobar ta kashe.
A awanni 24 da suka gabata mutane 669 Corona ta kama a Ecuador wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu a kasar zuwa dubu 478,615. Wadanda suka warke kuma sun kai mutane dubu 443,880.