Mutane miliyan 733 sun gamu da ibtila'in yunwa a bara - MDD

Mutane miliyan 733 sun gamu da ibtila'in yunwa a bara - MDD

Sabon rahotan da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya biyar da ke maida hankali kan al’amura da suka shafi abinci suka wallafa wannan Laraba, ya ce ɗaya daga cikin mutane 11 na duniya ko ɗaya cikin ƴan Afirka biyar sun fuskanci bala’in yunwa a shekarar da ta gabata.

Rahoton ya nuna cewa samun isasshen abinci ya kasance babbar ƙalubale ga kusan mutane biyan 2 da miliyan 330 a duniya, inda suka fuskanci tsanani ko matsakaicin ƙarancin abinci a shekarar ta 2023.

Rahotan ya kara da cewa, wannan adadi bai canza sosai ba kan yanayin da aka gani a shekarar 2020 sakamakon tashin hankali da aka gani saboda annobar kororana.

David Laborde, Darektan Cibiyar Noma na Abinci ta Duniya, ya ce magance matsalar ya ta’allaka ne ga shugabannin siysa, da kuma irin kuɗin da ake warewa kan matsalar.

Jami’in ya ce muddun al’amura suka ci gaba da tafiya a haka, to nan da shekara ta 2030 sama da mutane miliyan 582 ne zasu fuskanci bala’in yunwa a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)