A kalla mutane miliyan 51,6 ibtila'o'i suka shafa a duniya baki daya a wannan shekarar.
Tarayyar Kungiyoyin Red Crescent da Red Cross sun bayyana cewar sauyin yanayi ya janyo ibtila'o'i irin su ambaliyar ruwa, fari, guguwa da gobarar daji inda a kalla mutane miliyan 51,6 suka illatu.
Shugaban Tarayyar Francesco Rocca ya sanar manema labarai game da bincike da nazarin da suka yi kan matsalolin da sauyin yanayi ya janyo.
Rocca ya ja hankali da cewar annobar Corona (Covid-19) ta sake kara yawan illar da ibtila'o'in suka yi ga dan adam, kuma ya zuwa yau guguwa 92 daga cikin 132 da suka afku a 2020 sun faru ne a lokacin da ake fama da Corona.
Francesco Rocca ya ci gaba da cewa, ana shan wahalar isa ga al'umun da wannan matsala ta shafa kuma a duniya gaba daya a kalla mutane miliyan 51,6 ne suka tagayyara.
Rocca ya kara da cewar gobarar daji kuma ta shafi mutane miliyan 2,3 a duniya.