Amurkawan da ke zaben na wuri na yin tattaki ne zuwa wuraren da aka tanada don kaɗa kuri’unsu, yayin da wasu kuma ke aikewa da kuri’un ta sakwannin imel
Tuni dai adadin masu kaɗa ƙuri’un na wuri ya haura mutane miliyan 18 a Amurkan, adadin da ake sa ran zai cigaba da ƙaruwa, idan aka yi la’akari da jimilar ƙuri’u sama da miliyan 150 da aka kaɗa yayin zaɓen shekarar 2020.
Kaɗa ƙuri’un na wuri da Amurkawan ke yi na gudana ne a jihohin ƙasar 47, ciki har da Georgia, wadda ke cikin jihohi bakwai masu tasiri wajen sauya alƙaluman babban zaben na Amurka.
A baya bayan nan, sakataren gwamnatin Georgia Brad Raffensperger ya shaida wa manema labarai cewa, kashi 70 cikin 100 na ‘yan jihar ake sa ran za su kaɗa ƙuri’unsu a kafin ranar zaɓen shugabancin Amurka da ke tafe wato biyar ga watan Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI