Mutane kusan dubu 1,300 girgizar kasa ta yi ajali a Haiti

Mutane kusan dubu 1,300 girgizar kasa ta yi ajali a Haiti

A kalla mutane dubu 1,297 ne suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 7,2 da ta afku a ranar Asabar a gabar tekun Haiti.

Mahukuntan kasar sun bayyana cewa, an samu rusau da yawa kuma ana ci gaba da ciro mutane daga karkashin buraguzan gine-ginen.

Kungiyar Kare Fararen Hula ta Haiti ta shaida cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa ya karu zuwa mutane dubu 1,297, wadanda suka jikkata kuma sun haura dubu 5,700.

Gwamnatin kasar da ta fuskanci rusau da motsawar kasa ta yi kira ga kasashen duniya da su taimaka musu.

Firaministan haiti Ariel Henry ya sanar da cewai an samu asara sosai sakamakon ambaliyar ruwan.

Henry ya sanar da saka dokar ta baci ta wata guda a kasar.

 


News Source:   ()