Mutane huɗu sun mutu a harin ta'addanci a Turkiyya

Mutane huɗu sun mutu a harin ta'addanci a Turkiyya

Shugaban Turkiyya wanda ke ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, daidai lokacin da harin ya faru ya yi tir da harin da ya kira na ta’addanci.

Ministan cikin gida na kasar, Ali Yerlikaya ne dai ya tabbatar da faruwar wannan al’amari a shafinsa na X, inda ya ce an jiyo amon harbe-harbe da karar fashewa bam.

Harin dai ya faru ne a lokacin da ake gudanar da wani babban bikin baje kolin kasuwanci na kayayyakin tsaro a Istanbul, wanda babban jami'in diflomasiyyar Ukraine, Andrii Sybiha ya ziyarci wurin.

Har yanzu dai ba a san musabbabin fashewar bam da kuma wadanda suka kai harin ba.

Sai dai kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa harin na kunar bakin wake ne, inda aka yi garkuwa da wasu mutane.

Shaidu sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa jami’an kai daukin gaggawa sun kai wasu daga cikin ma’aikatan da ke cikin ginin zuwa wani matsuguni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)