Hukumomin Ukraine sun bayyana cewa "ana gudanar da aikin ceto a gundumar Dnipro bayan harin makami mai linzami,Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a kan Telegram, ya na mai bayyana takaincin sa tareda shigar da kira ga kasashe aminan Ukraine na ganin sun kawo mata dauki.
Gwamnan yankin, Serguiï Lyssak, a nasa bangaren ya ba da rahoton cewa mutane 21 sun jikkata, takwas daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
Serguiï Lyssak ya karasa da cewa mutanen da lamarin ya ritsa da su "na fama da raunin, lalacewar gabobi ciki har da karaya."
Birnin Dnipro, wanda ke da mazauna 970,000 kafin wannan yakin,said ai yanzu haka da dama daga cikin mazauna garin ne suka kaura zuwa wasu yankuna.
A ranar 21 ga Nuwamba Rasha ta harba makami mai linzami na gwaji mai suna "Orechnik".
Wannan harin ya shafi wata babbar masana'antar soji, PivdenMach, wacce ke kera abubuwan da ake amfani da su na makamai masu linzami.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI