Tun daga farkon shekarar 2020 zuwa yau mutane dubu 95 sun yi hijira a Yaman sakamakon Ibtila'o'i, yake-yake da annobar Corona (Covid-19).
Hukumar Gudun Hijira ta Kasa da Kasa (IOM) ta fitar da wata rubutacciyar sanarwa cewa daga watan Janairu zuwa yau an samu gudun hijira da yawa a Yaman.
Sanarwar ta ce Yamanawa da suka ji tsoron ambaliyar ruwa, yaki da annobar Covid-19 sun bar matsugunansu tare da guduwa wasu yankunan.
Sanarwar ta ce "Yamanawa dubu 94 da 488 sun bar matsugunan. Sun hada da iyalai dubu 17,748."
A Yaman da aka dauki tsawon shekaru ana yakin basasa, 'yan tawayen Houthi da Iran ke taimakawa a watan Satumban shekarar 2014 sun kwace iko da San'a Babban Birnin Kasar da wasu yankunan. Kawancen Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya kuma sun fara kai wa mayakan na Houthi hare-hare ta sama a watan Maris din shekarar 2015.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sakamakon yakin basasar Yaman kaso 8 na al'umar kasar na bukatar taimakon jin kai.