A duniya baki daya, annobar Corona (Covid-19) ta yi ajalin jimillar mutane dubu 833,875 daga cikin mutane miliyan 24 da dubu 570 da ta kama, wadanda suka warke kuma sun kai mutane miliyan 17.
A Indiya, mutane 57 sun sake rasa rayukansu wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa dubu 61,529. A awanni 24 da suka gabata an sake samun mutane dubu 77,266 da suka kamu da Corona inda a yanzu ake da adadin masu dauke da ita a Indiyasu miliyan 3,387,500.
A nahiyar Afirka kuma cutar da ta sake yin ajalin mutane 254 wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa dubu 28,910. Wadanda suka kamu da cutar a nahiyar kuma sun kai mutane miliyan 1 da dubu 225. Ya zuwa yau Afirka ta Kudu ce ke da mafi yawan rasa rayuka da mutane dubu 13,628, sai Masar da mutane dubu 5,342 inda Aljeriya ke biye mata baya da mutane dubu 1,475.