A kalla mutane 28 ne suka rasa rayukansu, wasu 78 suka jikkata sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a Bagdad Babban Birnin Iraki.
'Yan sanda sun bayyana cewar, fashewar ta afku a wata kasuwa da ke dandalin Tayran na Bagdad.
Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu saboda wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.
An bayyana cewar, an kai harin da rigar tayar da bama-bamai.