Rahotannin farko sun bayyana cewa, a kalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar wasu abubuwa a filin tashi da saukar jiragen saman garin Aden na Yaman.
Fashewar ta afku a bangaren zaman fasinjoji na filin jirgin saman Aden a lokacin da sabbin mambobin majalisar zartarwar kasar suke shiga Yaman.
Labaran da aka fitar a tashar Al Arabiyya da ke Saudiyya na cewa, jim kadan bayan saukar jirgin sama dauke da mambobin majalisar zartarwar sabuwar gwamnatin Yaman aka harba bama-bamai 3 tare da bude wuta a filin tashi da saukar jiragen saman na Aden.
Firaministan Yaman Muin Abdulmalik ya fitar da rubutacciyar sanarwa ta shafinsa na sada zumunta cewa, jami'an majalisar zartarwar na cikin koshin lafiya.
Ya ce "Wannan hari na ban tsoro da aka kai wa filin tashi da saukar jiragen saman Aden, wani bangare ne na yaki da ake yi da jama'ar Yaman."
Abdulmalik ya kuma kara da cewar sun dauki matakin ci gaba da aiyuka don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da kawo karshen juyin mulkin da 'yan tawayen Houthi da Iran ke taimakawa suka yi.
Ministan Yada Labarai na sabuwar gwamnatin Yaman Muammer Al-Iryani ya sanar da cewa, wannan hari na ban tsoro na ta'addanci ba zai hana su gudanar da aiyukansu ba."