An kashe mutane biyu a wani harin bam a wata kasuwa a Mogadishu, babban birnin Somaliya.
Jami'in 'yan sandan Mogadishu Abdifatah Hassan ya sanar da cewa, an kai harin bam a wata karamar kasuwa da ke Ex-control Afgooye, a Mogadishu babban birnin kasar.
Da yake bayyana cewa mutane 2 sun rasa rayukansu a harin, Hassan ya ce,
"Muna zargin wanda ya kai harin dan kunar bakin wake ne sanye da rigar kunar bakin wake,"
Hassan ya kara da cewa an tura jami'an tsaro zuwa wurin kuma an fara gudanar da bincike akan lamari.
A gefe guda kuma, a cikin labarai a jaridun kasar, an sanar da cewa ana kula da mutane 8 da suka jikkata a harin.
Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Kungiyar ta'adda ta Al-Shabab ta kan shirya kai hare-hare kan jami'an tsaro da matsugunan fararen hula a Somaliya.