Fararen hula 5 ne suka mutu a wani harin bam a lardin Kandahar da ke kudancin Afghanistan.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na Kandahar, Cemal Nasır Barikzey ya ce, bam din da aka sanya a gefen titin Argistan na Kandahar ya tashi ne yayin da motar da ke dauke da fararen hula ta wuce yankin.
Da yake bayyana cewa fararen hula 5 ne suka rasa rayukansu, Barikzey ya zargi kungiyar Taliban da kai harin.
Sai dai kuma, har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.