Rahoton wanda hukumar raya birane ta Majalisar ɗinkin duniya UNDP ta fitar a yau Alhamis ya nuna yadda mutanen biliyan 1 da dubu 100 ke rayuwa a halin matsanancin karancin abinci, rashin lantarki baya ga rashin tsaftataccen ruwan sha ko na amfani, kuma galibinsu na a ƙasashen da ke fama da ko dai yaƙi ko kuma rikicin ƙabilanci ko na siyasa sai kuma masu fama da ayyukan tsageru ko ƴan ta’adda.
Bayan tattara bayanan wani bincike da UNDP ya gudanar a ƙasashe 112 ne tsakanin mutum biliyan 6 da miliyan 300, ya tabbata cewa fiye da mutum biliyan guda da miliyan 100 na a hali na matsanancin talauci da ke da nasaba da tashe-tashen hankula, lamarin da ya sake jefa duniya a talauci bayan da rahoton ke cewa akwai kuma wasu mutum miliyan 455 da suma ka iya faɗawa a talauci kowanne lokaci daga yanzu.
Shugaban hukumar ta UNDP Achim Steiner ya ɗora alhakin tsanantar talaucin kan tashe-tashen hankulan da ake gani a sassan duniya wanda ya tilasta mutane da dama tserewa daga matsugunansu da rayuwa da cikin ƙasƙanci a yankunan da suka samu kansu.
Rahoton ya ce akwai matasa da ƙananan yara aƙalla miliyan 584 ƴan ƙasa da shekaru 18 da ke rayuwa a matsanancin talauci adadin da ke wakiltar kashi 27.9 na yaran da ke duniya mafi yawa idan an kwatanta da yawan manyan da ke fama da talaucin wanda ke wakiltar kashi 13.5.
Rahoton ya ce kashi 83.2 na matalautan duniya na rayuwa ne a ƙasashen kudu da saharar Afrika da kuma kudancin Asiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI