Mutane akalla 135 ne suka mutu a Labanan

Mutane akalla 135 ne suka mutu a Labanan

Mutane akalla 135 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar da ta afku a ranar Talatar nan a tashar jiragen ruwa da ke Beirut Babban Birnin Labanan.

Ministan Lafiya na Labanan Hamad Hasan ya shaida cewar "Sakamakon fashewar da ta afku a tashar jiragen ruwa ta Beirut mutane akalla 135 sun mutu, kuma wasu kusan dubu 5 sun jikkata inda da dama kuma suka makale a karkashin gine-ginen da suka rushe."

Game da batun za a fuskanci matsalar garin fulawa da burodi a kasar sakamakon fashewar, Ministan Kasuwanci da Tattalin Arziki na Labanan Raul Name ya ce sun dauki dukkan matakan ganin hakan ba ta faru ba.

Majalisar Tsaro ta Labanan ta aiyana Beirut a matsayin yankin ibtila'i.


News Source:   ()