Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a cikin ambaliyar ruwa da ta afku sakamakon mamakon ruwan sama da aka kwashe kwanaki ana yi a Beljiyom, ya haura zuwa 9.
Mamakon ruwan saman ya fi shafar yankuna kamar Liege, Verviers, Spa, Namur da Limburg da ke gabashin kasar. Mahukuntan yankin sun sanar da cewa mutane 9 sun rasa rayukansu a ambaliyar a wadannan garuruwan da kuma kauyukan da ke kusa da su.
An bayyana cewa mutane 4 sun bata a yankin kuma kungiyoyin bincike da ceto suna ta kokarin nemo wadannan mutanen.
Gidaje da dama sun rushe a yankin sakamakon ambaliyar, dubban gidaje da wuraren kasuwanci sun cika da ruwa. Wasu garuruwa da kauyuka ba su da wutar lantarki tun jiya. An sanar da cewa ruwan sha ya gurbata a wasu biranen, musamman a Verviers. Ambaliyar ta kuma tafi da motoci da yawa.
Yayinda manyan hanyoyi da yawa a gabashin kasar suka kasance a rufe saboda ambaliyar, an dakatar da aiyukan jiragen kasa da yawa.
Ana ci gaba da aiyukan ceto a Luxembourg don gano wadanda suka makale a cikin ambaliyar. An kwashe mutane daga wasu kauyuka a yankin.