Mutane 81 ne suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ta afku a Tsibirin Sulawesi na Indonesiya.
Ana ci gaba da aiyukan ceto a yankin na Yammacin Sulawesi da girgizar kasa ta afku.
A aiyukan da ake yi, an sake ciro jikkunan mutane 8 wandah akan ya kara yawan wadanda suka mutu zuwa 81, 70 a Mamuju da kuma 11 a Majene.
Sakamakon girgizar kasar, gidaje kusan 200 da suka hada da na gwamnati sun samu matsala. Ana ci gaba da aiyukan ceto a gidajen da suka rushe baki daya.
Mahukunta sun ce, ana kuma ci gaba da kula da mutane 253 da suka jikkata a asibitocin yankin, kuma wadanda aka kwashe daga yankin sun kai dubu 28.
A ranar 15 ga Janairu ne Hukumar Kula da Yanayi ta Indonesiya ta bayyana afkuwar girgizar kasa mai karfin awo 6,2 Tsibirin Sulawesi.
Girgizar ta afku a karshin kasa da zurfin kilomita 10.