Mutane 62 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin kasa da ya afku a ranar Lititinin din da ta gabata a jihar Sindh da ke Pakistan.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun bayyana an sake gano gawarwakin mutane 11 wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutane 62.
Sama da mutane 100 ne suka jikkata sakamakon hatsarin jirgin kasan.
A gefe guda Ministan Sufurin Jiragen Kasa na Pakistan Muhammad Azam Han ya ziyarci wajen da hatsarin ya afku, ya ce an fara gudanar da bincike, kuma za a hukunta wadanda suka janyo afkuwar hatsarin.
A safiyar ranar Litinin din nan ne taragon wani jirgin kasa ya cire tare da yin karo da wani jirgin da ke tahowa daga daya bangaren a layin dogo da ke jihar Sindh.