Mutane 5 daga iyali 1 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar wani karamin jirgin sama a jihar Georgia da ke Amurka.
Labaran da jaridun Amurka suka fitar sun ce jirgin saman samfurin Piper 31T mai injina 2 ya tashi daga jihar Florida zuwa Indiana, kuma ya fado a jihar Georgia.
Mahukuntan Amurka sun ce matukin jirgin Larry Pruitt, matarsa da 'ya'yansa 3 sun mutu a hatsarin.
An bayyana cewar iyalan sun tafi halartar wani taron Jana'iza ne a lokacin da hatsarin ya afku.