Mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin sama da wani jirgin sama dauke da 'yan wasan saukar lema ya yi yayin sauka a yankin Saberiya na Rasha.
Sanarwar da Ma'aikatar Bayar da Agajin Gaggawa ta Rasha ta fitar ta ce, jirgin saman samfurin L-410 da ke dauke da masu wasannin lema ya fado a yankin Kemerovo na Saberiya.
Matukin jirgin ya yi kokarin saukar da shi ta karfi a filin tashi da saukar jiragen sama na Tanay wanda sakamakon sauka da fika-fikin hagu hatsarin ya afku.
Sanarwar da aka fitar daga fadar gwamnan Kemerovo ta ce, mutane 4 da suka hada da matukan jirgin 2 sun rasa rasa rayukansu, wasu 15 kuma sun samu raunuka inda 4 daga cikinsu suke cikin mawuyacin hali.