Haɗarin na jiya Larabar shi ke matsayin haɗarin jirgi da ya faru a shekarun baya-bayan nan da aka samu kaso mai yawa na fasinjan da suka tsira da rayukansu.
Ma’aikatar ayyukan agaji ta Kazakhstan ta shaidawa kamfanin dillanci labarai na Rasha RIA Novosti cewa an kai ɗaukin gaggawa ga waɗanda haɗarin ya rutsa da su inda yanzu haka aka kai mutane 29 asibiti don karɓar kulawar gaggawa ciki har da ma’aikatan jirgin mutum 5.
RIA ya ruwaito cewa nan ta ke an ɗauki gawarwakin mutane 4 ciki har da matuƙan jirgin biyu.
Bayanai sun ce jirgin na kan hanyarsa ta isa Rasha ne amma tangarɗar inji ta tilasta shi ƙoƙarin saukar gaggawa gabanin faɗuwarsa a tazarar kilomita 3 kafin isa inda tun farko ya tsara saukar gaggawar.
A tashin farko mahukuntan Kazakhstan sun ce mutane 25 ne suka tsira da rayukansu gabanin ƙara adadin daga bisani zuwa 29 ciki har da yara 3, yayinda wasu 38 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI