Mutane 38 guguwa da dusar kankara suka yi ajali a Japan

Mutane 38 guguwa da dusar kankara suka yi ajali a Japan

Ya zuwa yanzu mutane 38 ne suka rasa rayukansu sakamakon guguwa da dusar kankara da suka zuba a Japan.

Karin mutane 8 sun sake mutuwa yayinda wasu 270 a garuruwan Niigata, Toyama,Ishikawa, Fukui da Gifu da ke Japan sakamakon guguwa da zubar dusar kankarar.

Hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutane 38.

Sakamakon rashin kyawun yanayi an dakatar da safarar jiragen sama da dama.

Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta ce, a wasu yankunan kasar tudun dusar kankarar ya kai tsayin mita guda, sun kuma gargadi jama'a da kar su fita waje.

Hukumar ta ce, tun shekarar 1986 a karon farko yawan dusar kankara ya kai  santimita 120 a garin Toyama.


News Source:   ()