Mutane 30 sun mutu sakamakon wani abun fashewa da ya tashi a Baghdad

Mutane 30 sun mutu sakamakon wani abun fashewa da ya tashi a Baghdad

An ba da rahoton cewa mutane 30 sun rasa rayunkansu kuma wasu 60 sun samu raunuka sakamakon fashewar wani abu a cikin wata kasuwa a Baghdad, babban birnin Iraki.

A cewar bayanan da aka samu daga majiyoyin lafiya na gwamnati, fashewar ta afku a kasuwar Al-Vahilat da ke yankin Sadr na gabashin Baghdad.

A cewar rahotannin farko, mutane 30 sun mutu sannan wasu mutane 60 sun samu raunuka a fashewar da ta afku a jajibirin ranar Eid-al-Adha. Daga cikin wadanda suka mutu har da mata da yara kanana.

Duk da yake ba wanda ya dauki alhakin kai harin, an fara gudanar da bincike kan lamarin.

Cibiyar yada labarai ta Ma’aikatar Tsaro ta bayyana cewa fashewar ta ta’addanci ce.

Firaminista Mustafa al-Kazemi ya kuma bayar da umarnin tsare kwamandan da ke kula da yankin da aka kai harin.


News Source:   ()