Mutane 30 ne suka bata a ambaliyar ruwa da ta afku sakamakon mamakon ruwan sama a yankin Eifel da ke jihar Rhineland-Palatinate ta Jamus.
A cewar labaran SWR, wani sashe na Tashar Talabijin ta Farko ta Jamus ARD, gine-gine 6 sun rushe a garin Schuld da ke kusa da garin Adenau.
A cikin labaran da aka bayyana cewa ana neman mutane 30, an kuma rawaito cewa karin gine-gine 25 na cikin hatsarin rugujewa.
An bayyana cewa lamarin na da hatsari saboda ambaliyar ruwa a yankin Bitburg-Plum, an lura da cewa mutane 5 a garin Waxweiler sun makale a cikin wani gida da ruwa ya kewaye kuma kungiyoyin ceto sun gaza isa gidan da jirgin ruwa.