Mutane 25 ne suka rasa rayukansu sakamakon rushewar wani gini mai hawa 4 a kasar Indiya.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce a Mumbai babban birnin jihar Maharashtra ne gini mai hawa 4 ya rushe a ranar 21 ga Satumba inda a yanzu aka sake gano gawarwakin mutane 15.
Mahukunta sun ce a kalla akwai karin mutane 8 a karkashin ginin.
Firaministan Indiya Narendra Mondi ya mika sakon ta'aziyya ga makusantan wadanda suka mutu a lamarin.